Connect with us

News

NAPTIP Ta Kama Mutumin Da Ake Zargi Da Safarar Yara 10 A Jalingo

Published

on

Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) reshen Taraba ta kama wani mutum da ake zargi da safarar yara 10 a Jalingo, babban birnin jihar.

Kwamandan NAPTIP a Taraba, Bako Amos, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 11 na safe, bayan samun bayanan sirri.

Advertisement

Gwamnan Katsina Zai Gina Gidaje 3,750 A Radda Da Kankiya Kan Naira Biliyan 155

Amos ya bayyana cewa jami’an hukumar sun yi aiki tare da Misis Sarah Ishaya, Mai Bai wa Gwamnan Taraba Shawara ta Musamman kan Safarar Mutane, wajen kama wanda ake zargin a Kurmi Park, Jalingo, a lokacin da ake shirin tura yaran zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba.

Advertisement

Ya kara da cewa yaran da wanda ake zargin suna hannun NAPTIP, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan lamarin.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending