Connect with us

News

Yan Ta’adda Sun Kona Ofishin ‘Yansanda, Coci Tare Da Garkuwa  Da Wasu A Neja

Published

on

Wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne , a safiyar Lahadi, sun kona ofishin ‘yansanda da cocin UMC a garin Sokombara da ke karamar hukumar Agwara ta jihar Neja.

Rahotanni na nuni da cewa ‘yan bindigar sun kuma kashe wata tsohuwa, sun sace mutane biyar daga cikin al’ummar sannan suka sace kayan abinci da sauran kayayyaki na mutanen kauyen.

Advertisement

Yaro Ɗan Shekara Uku Ya Rasa Ransa Sakamakon Faɗuwa Cikin Rijiya A Kano

Da yake tabbatar wa LEADERSHIP lamarin, jami’in hulda da jama’a na ‘yansandan (PPRO), SP Wasiu Abiodun, ya ce; “‘Yan bindiga dauke da makamai sun mamaye al’ummar Agwara, sun kai hari ofishin ‘yansanda inda jami’an suka yi artabu da su, daga nan sai ‘yan bindigar suka harbo abun fashewa a kan ofishin, bayan sun yi galaba a kan jami’an.”

Advertisement

Wannnan sabon harin yana cikin manyan hare-hare guda uku da aka kai wa al’ummomin Agwara tun bayan sacewa da sakin yaran makaranta da ma’aikata na Papiri a ƙarshen 2025 a wannan ƙaramar hukumar ta Agwara da ke jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending