News
Gamayyar ’Yan Kasuwar Man Fetur Ta Bukaci FCCPC Ta Binciki Zargin Da Akewa Matatar Dangote Na Mamaye Dukkan Damarmaki
Wata gamayyar ’yan kasuwar man fetur a Najeriya ta bukaci Hukumar Kula da Gasa da Kare Haƙƙin Masu Sayen Kayayyaki ta Ƙasa (FCCPC) da ta gaggauta bincike kan zargin da ake yi wa Matatar Dangote na mamaye kasuwar man fetur ta hanyar amfani da tsarin farashi da ka iya tauye gasa.
A cewar ƙungiyar, salon da matatar ke amfani da shi wajen kayyade farashin man fetur na iya hana gasa ta gaskiya a kasuwa, tare da jefa harkokin kasuwanci cikin rashin tabbas da ruɗani.
Kotu Ta Yankewa Tsohon Manajan Daraktan Bankin NEXIM Hukuncin Daurin Shekaru 490
’Yan kasuwar sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, inda suka jaddada cewa an kafa FCCPC ne domin dakile duk wani salo na kasuwanci da zai iya cutar da adalci a kasuwa, tare da kare masu sayen kaya daga duk wani nau’in cin zarafi.
Sun zargi matatar da cin gajiyar rinjayen da take da shi a kasuwa, inda suka ce ana sayar da man fetur a farashi guda, daga bisani kuma a sanar da rage farashi ba tare da mayar da kudin ga ’yan kasuwar da suka riga suka saya ba.
A cewarsu, wannan lamarin ya fi shafar manyan masu saye, inda bayan sun ɗora kayansu ne ake rage farashin, lamarin da ke rage musu kwarin gwiwar yin sayayya mai yawa a nan gaba.
Ƙungiyar ta kara da cewa irin wannan dabi’a na iya kaiwa ga kafa farashi ko tsaurara farashi a kasuwa, abin da dokokin Najeriya suka haramta.
Saboda haka, ’yan kasuwar sun bukaci FCCPC tare da sauran hukumomin da ke kula da harkokin man fetur da su hada kai wajen gudanar da cikakken bincike, tare da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da gasa ta gaskiya da kare muradun masu amfani da kayayyaki.
