News
KANO: Ma’aikatar Kananan Hukumomi da NULGE Sun Shirya Taron Kara Ilimi ga Ma’aikata
Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano tare da hadin gwiwar NULGE (Nigeria Union of Local Government Employees) sun gudanar da wani muhimmin taro na horaswa domin karfafa hadin gwiwa da inganta kwarewar ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar.
Taron, wanda aka shirya a daidai lokacin da aka cika shekara guda da gudanar da zaben shugabannin kungiyar a matakin jiha, ya mayar da hankali ne kan kara ilimi da fahimtar hanyoyin gudanar da aiki yadda ya kamata domin bunkasa ingancin ayyukan ma’aikata.
Shugaban NULGE na reshen Jihar Kano, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin koyar da ma’aikata sabbin dabarun aiki da za su kara inganta fahimta da ilimi a tsakanin ma’aikatan kananan hukumomi.
Ya ce irin wannan horo yana taimakawa wajen samar da kwararru masu nagarta da za su iya gudanar da ayyukansu yadda ya dace, tare da kara inganta ayyukan gwamnati a matakin kananan hukumomi.
A nasa jawabin, Shugaban NULGE na kasa, Hon. Aliyu Haruna, ya ce ba wannan ne karo na farko da ake shirya irin wannan horaswa ba, yana mai jaddada cewa Jihar Kano na daga cikin jihohin da ke bai wa ma’aikata horo da bita akai-akai domin inganta ayyukan yau da kullum.
Ya kara da cewa ci gaba da horas da ma’aikata na daga cikin muhimman matakan da ke tabbatar da nagartar hidimar gwamnati ga al’umma.
Wakiliyarmu Safiya Muhammad Usman, wadda ta halarci taron, ta rawaito cewa Shugaban NULGE na reshen Jihar Kaduna, Kwamared Rayan Isa, ya yabawa gwamnatin Kano bisa goyon bayan da ta bayar wajen gudanar da taron.
Hakazalika, ya yi kira ga ma’aikatan kananan hukumomi da su yi amfani da ilimin da suka samu a taron wajen koyar da takwarorinsu da ba su samu damar halarta ba, domin fadada anfani da horon ga kowa.
