News
KARUWAR YARA MASU GARARAMBA A TITUNA: Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama Ta Yi Gargadin Babbar Barazanar Tsaro
Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta kasa da kasa reshen Najeriya ta yi gargadi cewa karuwar yaran da ke rayuwa a tituna a manyan biranen kasar na zama babbar barazana ga hakkin yara da kuma tsaron kasa baki daya.
A cikin sanarwar manema labarai da ta fitar, kungiyar ta bayyana cewa matsalar yaran titi ba wai al’amari ne na talauci ko jin kai kawai ba, illa lamarin da ke kara rikidewa zuwa barazana ga zaman lafiyar al’umma da makomar kasa.
Fiye Da Kananan Yara Miliyan Biyu Ke Gararamba A Titunan Kano — NGO
Kungiyar ta ce daga mahangar tsaro, barin yara ba tare da kulawa da tsari ba kan samar da dama ga masu aikata laifi su yi amfani da su.
Ta bayyana cewa yara masu rayuwa a tituna na iya fadawa cikin:
kungiyoyin daba da aikata kananan laifuka,safarar miyagun kwayoyi,tayar da rikice-rikice, da lalacewar makoma sakamakon rashin kulawa da jagoranci.
A cewar kungiyar, yaron da aka bari ba tare da kulawa ba a yau, na iya zama barazana ga zaman lafiyar al’umma a nan gaba.
Sanarwar ta kara da cewa rayuwar titi na tauye muhimman hakkokin yara, ciki har da hakkin samun ilimi, kariya daga cin zarafi da amfani da su ba bisa ka’ida ba, da kuma hakkin rayuwa cikin mutunci.
Kungiyar ta jaddada cewa titi ba gida ba ne, bara ba tarbiyya ba ce, kuma rayuwar titi ba makomar yaro ba ce.
Kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su ayyana matsalar yaran titi a matsayin dokar ta-baci ta kasa, tare da gudanar da cikakken bincike da kididdiga, da samar da shirye-shiryen mayar da yara makaranta ko koyon sana’a.
Haka kuma ta bukaci a karfafa cibiyoyin kula da yara marasa gata, a hukunta masu amfani da yara wajen bara ko cin zarafi, da kuma kara hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, ma’aikatar jin kai, shugabannin gargajiya da kungiyoyin farar hula.
Kungiyar ta ce batun ya wuce siyasa, domin yana da nasaba kai tsaye da makomar kasa.
Ta kuma yi gargadin cewa kasa da ba ta kare yaranta ba, tana lalata tubalinta ne da kanta, tana mai kira ga daukar mataki cikin tsari, kwarewa da jin kai.
