News
Wasu Gungun Fusatattun Matasa Sun Kone Wanda Ake Zargi Da Satar Babur
Wani mutum da ake zargi da ƙoƙarin satar babur ya rasa ransa bayan wasu gungun fusatattun matasa sun kai masa hari tare da ƙone shi a birnin Makurdi, babban birnin Benue State.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026, kusa da harabar Baptist Secondary School, Achusa, inda ake zargin mutumin ya yi yunƙurin ƙwace wani babur.
Jami’an Hukumar DSS Sun Shigar Da El-rufai Ƙara Kan Datsar Kiran Wayar Nuhu Ribadu
Mutanen da suka ga abin ya faru sun ce jama’a sun taru bayan kama wanda ake zargin, lamarin da ya rikide zuwa wata kala mara dadi. Rahotanni sun ce taron mutanen sun kai masa hari kafin daga bisani aka banka masa wuta.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, ba a tabbatar da sunan mutumin ba, kuma babu sanarwa a hukumance kan ko an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.
Hukumomin tsaro sun sake gargadin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, suna mai jaddada cewa duk wanda ake zargi da aikata laifi ya kamata a miƙa shi ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike da kum gurfanarwa a gaban kotu.
A cewar hukumomin, abin da ake kira jungle justice na tauye bin doka da oda, kuma yana iya janyo mutuwar marasa laifi tare da ƙara haddasa rashin tsaro a cikin al’umma.
