News
Shugaba Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri Da Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Ganawar, wadda ta gudana a Juma’ar nan ta kasance karkashin tsauraran matakan tsaro, ba tare da bayyana maƙasuɗinta ba ga jama’a.
Hakan ya haifar da cece-kuce da hasashe a kafafen sada zumunta da kuma tsakanin masu nazarin harkokin siyasa.
Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga Fadar Shugaban Kasa ko gwamnatin Jihar Bauchi dangane da abin da aka tattauna a taron.
Gwamna Bala Mohammed, wanda jigo ne a jam’iyyar adawa ta PDP kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, ya isa Fadar Shugaban Kasa kamar yadda hotunan da ke yawo a intanet suka nuna ayarin motocinsa.
Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi a Najeriya, ciki har da kalubalen tsaro a wasu sassan Jihar Bauchi sakamakon hare-haren yan bindiga da suka raba mutane da muhallansu.
Haka kuma ana ci gaba da tattaunawa kan zaben 2027, sauya sheka tsakanin jam’iyyu, da kuma kokarin samar da hadin kai a tsakanin bangarori daban-daban.
A makonnin baya-bayan nan, Shugaba Tinubu ya rika ganawa da gwamnonin jihohi da dama, ciki har da na jam’iyyarsa ta APC da ma wasu daga bangarorin adawa, inda ake tattauna batutuwa kamar tsaro, gyaran tattalin arziki da siyasa.
