Connect with us

News

Badaƙalar N8.7bn: Kotu ta janye belin Malami da iyalinsa, ta tura su kurkuku

Published

on

Malami Wife Son 1024x572 1 768x429

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi hukuncin sabunta shari’ar tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa (AGF), Abubakar Malami bayan da ta yanke cewa ta koma sabuwa.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta ce tunda an sake gabatar da shari’ar a gaban kotun a matsayin sabuwa, dukkan hukuncin da aka yi baya har da belin da Alƙali Emeka Nwite ya bayar, an soke su.

Advertisement

Shugaba Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri Da Gwamnan  Bauchi, Bala Muhammad

Wannan hukunci ya nuna cewa wajibi ne tsohon ministan ya shigar da sabon ƙorafin neman beli kafin kotun ta duba yiwuwar amince wa sako shi da iyalansa.

Advertisement

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar da ƙarar gyararrun tuhume-tuhume guda 16 akan Malami, inda ta zarge shi da badaƙalar kuɗaɗe da mallakar wasu kadarori ba bisa doka ba da adadin kuɗaɗensu ya kai Naira biliyan 8.7.

A yayin shari’ar, lauyan da ke kare ɓangaren da ya shigar da ƙara, J.S. Okutepa ya shaida wa kotun cewa akwai buƙatar ta yi nazari akan sabbin tuhume-tuhumen da aka gabatar akan Malami.

Advertisement

Tuni dai Malami da ɗansa Abdulaziz Malami da kuma matarsa Asabe Malami suak musanta baki ɗaya zarge-zargen da ake musu.

Bayan haka ne Okutepa ya roƙi kotun da ta sanya wata rana domin sake zama akan shari’ar.

Advertisement

Yayin hukuncinta Alƙali Joyce ta ce tunda shari’ar ta koma sabuwa, dukkan hukuncin da aka yi a baya a kai an warware kamar yadda doka ta tanada.

Daga nan ne ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 6 ga Maris, 2026 domin zama akan sabon ƙorafin belin, sannan ta umarci a tsare Malami da Abdulaziz a kurkukun Kuje, ita kuma matar tasa a kai ta gidan gyaran hali na Suleja.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending