News
El-rufai Na Neman A Biya Shi Diyyar Biliyan 1 Daga Hukumar ICPC Da Sauran Hukumomin Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci a biya shi diyyar Naira biliyan ɗaya bayan zargin cewa an binciki gidansa da ke Asokoro a Abuja ba tare da bin ka’ida ba, ya ce matakin ya saɓa wa doka kuma ya tauye masa hakkinsa.
El-Rufai ya shigar da ƙara kan hukumar ICPC da kuma babban alkalin kotun majistare da babban lauyan gwamnatin tarayya, ya roƙi kotu ta duba lamarin.
Zamfara: Jami’an Tsaro Sun Kama Matashi Da Harsashi 800 Da Ya Ɓoye A Tankin Babur
Ya kuma nemi kotu ta tilasta wa hukumomin da ya kai ƙara su biya shi diyyar Naira biliyan ɗaya saboda abin da ya kira bincike ba bisa ka’ida ba.
Advertisements
