Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Kama Wata Mace Da Harsasai 884 A Kano

Published

on

IMG 20251231 WA0176

Jami’an rundunar sojin Najeriya ta Brigade ta 3 tare da hadin gwiwar jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kama wata mace da ake zargi da safarar makamai a Jihar Kano, yayin da take kokarin kai dimbin harsasai zuwa Jihar Zamfara.

‎Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama matar ne da misalin karfe 3:00 na asubahin ranar 14 ga watan Maris, bayan da jami’an tsaro suka samu bayanan sirri kan wani motsi na safarar makamai da ake zargin za a bi ta Kano da su.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Albashin Watan Maris Da Wuri Domin Sauƙaƙa Shirye-shiryen Sallah

‎Rahotanni sun ce matar na dauke da harsasai 884 na bindigar 7.62mm, wadanda ake zargin ta kwaso su daga Jihar Plateau domin kai su ga wasu kungiyoyin ‘yan bindiga da ke aikata ta’addanci a Jihar Zamfara.

Advertisement

‎A lokacin da aka kama ta, an ce tana tare da ’yarta mai shekaru 10, wadda ke tare da ita a lokacin safarar harsasan.

Advertisement

‎Binciken farko ya nuna cewa wasu mutane ne suka ba matar aikin kai harsasan zuwa Zamfara. A cewar majiyoyi, matar ta shaida wa jami’an tsaro cewa an ba ta naira dubu 50 , yayin da aka yi mata alkawarin za a biya sauran kudin bayan ta kammala aikin.

Advertisement

‎Rahotanni sun kuma ce matar ta amince cewa ta taba yin irin wannan aiki sau biyu a baya.

‎Jami’an tsaro sun mika wadda ake zargin tare da harsasan da aka kwato ga jami’an DSS domin ci gaba da gudanar da bincike.

Advertisement

‎Hukumomin tsaro sun ce bincike na ci gaba da gudana domin gano sauran mutanen da ke da hannu a safarar makaman, tare da kokarin dakile hanyoyin da ake bi wajen kai makamai ga ‘yan bindiga a jihohin da ke fama da matsalar tsaro.

 

Advertisement

PRNIGERIA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending