News
An Kama Wani Matashi Da Ke Bugar Da Marasa Lafiya Da Kayan Maye A Asibiti A Adamawa

Hukumomi a jihar Adamawa sun kama wani matashi da ake zargi da shiga asibiti yana bai wa marasa lafiya kayan maye a ɓoye.
Rahotanni na nuna cewa Ana zargin matashin da shiga asibitin koyarwa na Modibbo Adama da ke jihar Adamawa, inda yake bai wa marasa lafiya kayan maye a cikin lemu.
Matashin kan shiga asibitin ne kamar ya je duba mara lafiya, sai ya faki idon mutane ya bugar da masu jinya.
Bayan samun koke-koke daga cikin ma’aikatan asibitin da kuma wasu marasa lafiya, an fara sa ido a kan masu shiga da fita, wanda hakan ya kai ga kama wanda ake zargin.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro ko shugabannin asibitin da ke tabbatar da cikakken bayani kan lamarin.
A halin yanzu, ana ci gaba da bincike domin gano dalilin aikata wannan abu da kuma ko akwai wasu da ke da hannu a ciki.
