News
Ƙungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki
Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta gargadi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta aiwatar da sabon tsarin albashi da aka amince da shi ga malaman jami’o’i ko kuma ta fuskanci yiwuwar rufe jami’o’in gwamnati a duk fadin kasa.
Kungiyar ta bayar da wa’adin kwanaki hudu a ranar Alhamis, inda shugabanta, Christopher Piwuna, ya ce rashin daukar mataki a cikin wa’adin zai haifar da martani mai karfi.
Da yake jawabi a Jami’ar Sa’adu Zungur da ke Jihar Bauchi, Piwuna ya ce dole ne gwamnati ta fara biyan albashi a karkashin sabon tsarin albashi ba tare da wani bata lokaci ba.
Gargaɗin ya zo ne watanni bayan da ASUU da gwamnatin tarayya suka sake sanya hannu kan wata yarjejeniya a watan Janairu, da nufin warware takaddamar da ta daɗe tana tasowa da kuma hana yajin aikin da ke ci gaba da addabar tsarin jami’o’in Najeriya.
