News
Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Murabus
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya miƙa murabus daga mukaminsa.
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar.
Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Sabbin Lasisin shigo Da Mai Guda 6 Domin Rage Tsadar Man Fetur
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma bai wa ofishin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.
Sanarwar ta ce murabus ɗin ba yana nufin amincewa da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi ba, inda Mataimakin Gwamnan ya jaddada cewa yana da tsabtataccen tarihi a aikin gwamnati.
Sanarwar ta ƙara da cewa ya ɗauki matakin ne domin kauce wa rikice-rikicen siyasa da ka iya kawo tsaiko ga tafiyar gwamnati da ci gaban jihar.
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa zai mai da hankali wajen ƙarfafa ƙungiyar Kwankwasiyya da tsara dabarun siyasa gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta buƙaci magoya bayanta da al’ummar jihar da su kasance masu bin doka tare da ci gaba da goyon bayan shugabanci nagari.
