News
Kano: Gobara Ta Tashi A Gidan Mai, Ta Lalata Mota Da Wani Ɓangare Na Wurin
Wata gobara ta tashi a gidan man AYM Shafa da ke Kwanar FCE kan titin zuwa Gwarzo a jihar Kano, inda ta yi sanadin konewar wata motar dakon mai tare da wani ɓangare na gidan man.
Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe goma na daren ranar Asabar, lamarin da ya jawo firgici a tsakanin mazauna yankin.
Dakarun Soji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 38 A Borno
Sai dai jami’an kashe gobara sun kai dauki cikin gaggawa, inda suka yi nasarar shawo kan gobarar kafin ta bazu zuwa sauran sassan gidan man.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu bayanan asarar rayuka ko jikkata mutane sakamakon gobarar.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.
Advertisements
