Connect with us

News

Gawuna ya yi murabus daga shugabancin FMBN

Published

on

FB IMG 1774862969126

Tsohon ɗan takarar gwamna a Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi murabus daga mukaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Bankin Gidaje na Tarayya (FMBN).

A cikin wata takardar murabus mai ɗauke da kwanan watan 27 ga Maris, 2026, Gawuna ya ce matakin nasa ya fara aiki nan take, yana mai cewa ya yi hakan ne domin bin umarnin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na bukatar masu rike da mukaman siyasa su sauka bisa tanade-tanaden dokar zabe.

Gwamnan Borno  Ya Sallami Duk Kwaminishoninsa Nan Take

Ya ce: “Na dauki wannan mataki ne domin cikakken bin umarnin Shugaban Kasa da kuma dokar zabe gabanin wasu muhimman harkokin siyasa masu zuwa.”

Gawuna ya kuma gode wa Shugaba Tinubu bisa damar da aka ba shi na yin hidima, yana mai cewa mukamin ya ba shi damar bayar da gudunmawa ga ci gaban bankin da kuma kasa baki daya.

Haka kuma, ya bayyana cewa ya mika al’amuransa gaba daya ga Allah (SWT).

Advertisement

Ya kara da cewa zai tabbatar da mika ragamar aiki cikin tsari, bisa ka’idoji da dokokin da suka dace.

A gefe guda kuma, wasu rahotanni na nuni da cewa Gawuna na shirin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa ADC, bayan tattaunawa da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, kodayake babu wata sanarwa a hukumance kan hakan zuwa yanzu.

 

DAILY NIGERIAN 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending