News
An Sace jaririya Sabuwar Haihuwa A Hannun Mahaifiyarta Mai Shekara 19
Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace wata sabuwar jaririya daga hannun mahaifiyarta mai shekara 19 a unguwar Kidnawi 2 da ke Maraban Gurku, ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa
Lamarin ya faru ne a daren Asabar, inda rahotanni suka ce maharan sun kutsa cikin gidan matar da misalin ƙarfe 11 na dare yayin da take barci tare da jaririyarta.
Har Yanzu Kuɗin Kashewa Na Ɗalibai Na Wata-Wata N20,000 Ne Ba N25,000 —NELFUND
Mahaifiyar jaririyar, Aisha, ta shaida cewa wasu mutum biyu ne suka shiga ɗakin nata da ƙarfin tuwo. Ta ce ɗaya daga cikinsu ya riƙe ta a wuya tare da rufe mata baki, yayin da ɗayan ya ɗauki jaririyar ya tsere.
Ta ƙara da cewa ta yi ƙoƙarin neman taimako, amma makwabta ba su ji ihunta ba sai bayan da maharan suka gudu. A cewarta, mijinta ba ya gida a lokacin, domin yana jihar Legas.
Shugaban unguwar, Abubakar Yusuf Mai Anguwa Baƙo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an sanar da jami’an tsaro domin ɗaukar mataki.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani cikakken bayani daga hukumomin tsaro kan nasarar da aka samu wajen gano waɗanda ake zargi ko kuma inda jaririyar take.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, SP Rahman Nansel, ya ce bai samu rahoton lamarin a hukumance ba, yana mai kira ga mazauna yankin su tabbatar da cewa sun kai ƙorafi ga ‘yan sanda.
