Connect with us

News

Tsohon Gwamnan Kano, Abubakar Rimi, Ya Cika Shekaru 16 Da Rasuwa

Published

on

1680603344421

A yau ne ake cika shekaru 16 da rasuwar tsohon gwamnan Jihar Kano, marigayi Abubakar Rimi, wanda ya rasu a ranar 4 ga Afrilu, 2010.

An haifi Rimi a shekarar 1940 a ƙaramar hukumar Sumaila da ke Jihar Kano. Ya shugabanci jihar daga watan Oktoban 1979 zuwa Mayun 1983, a lokacin da ya gudanar da mulki mai cike da sauye-sauye a fannoni daban-daban.

Advertisement

JIGAWA: Uba Ya Fasa Aurar Da ‘Yarsa Ga Wani Saurayi Saboda Goyon Bayan Tinubu

Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne bayan wani hari da ‘yan fashi suka kai masa a kan hanyar Bauchi zuwa Kano. Ko da yake bai ji mummunan rauni ba a lokacin, daga bisani ya rasu sakamakon matsalolin zuciya.

Advertisement

A lokacin rayuwarsa, Rimi ya yi fice a siyasar Najeriya, inda aka san shi da kishin talakawa da kuma ƙoƙarin kawo sauyi, abin da ya sa ake masa laƙabi da “Limamin canji”.

Daga cikin muhimman ayyukan da ya aiwatar yayin mulkinsa sun haɗa da bunƙasa harkar ilimi ta hanyar tura ɗalibai ƙasashen waje, kafa hukumomin yaƙi da jahilci, da samar da Hukumar Ilmin Firamare.

Advertisement

Haka kuma ya ƙaddamar da shirye-shiryen samar da wutar lantarki a yankunan karkara, tare da kafa hukumomin kula da muhalli da tsara birane, baya ga tallafa wa ɗaliban sakandare da alawus na wata-wata.

Masu sharhi na ganin cewa har yanzu ana ci gaba da jin tasirin manufofin da ya aiwatar, musamman a ɓangaren ilimi da walwalar al’umma.

Advertisement

Ana dai ci gaba da tunawa da marigayin a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da suka taka muhimmiyar rawa wajen sauya fasalin mulki a Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending