Connect with us

Politics

Zaɓen 2027: Dr. Fatah Ya Fitar Da Manufofi Bakwai Domin Inganta Rayuwar Al’ummar Kano Ta Tsakiya ‎

Published

on

IMG 20260508 WA0019

Ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Dakta Mohammed Musa Zango, wanda aka fi sani da Dr. Fatah, ya bayyana cewa kudirinsa na neman wakiltar al’ummar mazabar ya samo asali ne daga nauyin da ke kansa na kawo ci gaba mai ma’ana da inganta rayuwar jama’a.

‎Dr. Fatah ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce shekaru da ya shafe yana hulɗa da al’umma a matakin ƙasa tare da gogewar da ya samu a fannoni daban-daban sun taimaka wajen tsara manufofin da zai aiwatar idan aka ba shi dama ya wakilci Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

Advertisement

Dr. Mohammed Musa Zango Ya Mayar Da Fom Din Takararsa Ga Uwar Jam’iyyar APC A Hukumance

‎Ya ce daga cikin manufofinsa akwai samar da ingantaccen wakilci da zai tabbatar da Kano ta Tsakiya na da murya mai ƙarfi da tasiri a Majalisar Ƙasa.

Advertisement

‎Haka kuma, ya ce zai mayar da hankali wajen bunƙasa harkar noma da tattalin arziki ta hanyar tallafa wa manoma, ƙarfafa sarrafa kayayyakin amfanin gona da samar da damar bunƙasa kasuwanci da sana’o’i.

‎A bangaren matasa da mata kuwa, Dr. Fatah ya yi alƙawarin ƙara samar da shirye-shiryen horaswa, tallafin sana’o’i da hanyoyin dogaro da kai musamman ga matasa da marasa galihu.

Advertisement

‎Ya kuma bayyana cewa inganta harkar lafiya na daga cikin manyan abubuwan da zai bai wa fifiko ta hanyar ƙarfafa cibiyoyin lafiya da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a faɗin Kano ta Tsakiya.

‎Dangane da ayyukan more rayuwa da masana’antu, ɗan takarar ya ce zai yi ƙoƙarin ganin an farfaɗo da manyan ayyuka irin su bututun iskar gas na AKK domin haɓaka masana’antu da bunƙasa tattalin arzikin yankin.

Advertisement

‎Haka zalika, ya ce samar da tsaftataccen ruwa da kuma farfaɗo da masana’antar yadi, wadda a baya ta kasance ginshiƙin tattalin arzikin Kano, na daga cikin muhimman manufofinsa.

‎Dr. Fatah ya ce waɗannan manufofi sun samo asali ne daga gogewa, tattaunawa da jama’a da kuma fahimtar matsalolin da ke addabar yankin, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da za a mayar da hankali wajen samar da sakamako mai amfani ga al’umma.

Advertisement

‎Ya ƙara da cewa zai ci gaba da tafiyar da shugabanci mai tsafta, kusanci da jama’a da kuma mayar da hankali wajen samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar Kano ta Tsakiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending