Connect with us

News

Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 

Published

on

IMG 20260512 WA02491 (1)

Ɗaga Kwamared Abbas Ibrahim 

 

Advertisement

Rikicin da ke girgiza kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ya kamata ya zama lokaci na zurfin tunani ga shugabannin Arewa maimakon ci gaba da fafutukar neman iko. An kafa ACF ne domin hada kan Arewacin Najeriya, kare muradunta, inganta zaman lafiya, da bayar da jagoranci kan al’amuran da suka shafi yankin. Idan rikice rikicen cikin gida suka rikide zuwa zarge zargen cin hanci, killace ofisoshi da ‘yan sanda, da rudanin kundin tsarin mulki, to martabar Arewa gaba daya ce ke tabarbarewa a idanun kasa baki daya.

Abin da ya fara a matsayin sabani tsakanin Kwamitin zartarwa a matakin kasa da Kwamitin Aminttattu, (BoT) yanzu ya bayyana wata babbar matsala ta rashin yarda da kungiyoyin dattawa a tsakanin matasan Arewa. Mutane da dama na zargin irin wadannan kungiyoyi sun zama na manyan ‘yan siyasa, iyalai, da tsofaffin abokan anfani kawai, yayin da ake tuna matasa ne kawai lokacin zabe ko gangamin siyasa, daga baya kuma a yi watsi da su.

Advertisement

Yadda Wata Mata Ta Banka Wa Mijinta Da Amaryarsa Da ‘Ya’yanta Guda Biyu Wuta A Kano ‎ ‎

Saboda haka, bai kamata rikicin ya kare da dakatarwa ko martanin dakatarwa kawai ba. Ya kamata ya zama wata dama ta yin gyara na gaskiya da sake farfado da kungiyar gaba daya.

Advertisement

Babban darasi da za a iya koya shi ne daga tsarin rundunar tsaro ta Amotekun na yankin Kudu maso Yamma. Duk da cewa manufarsu ta sha bamban, Amotekun ta samu nasara ne saboda hada tsofaffin jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki na al’umma, da sauran jama’a domin cimma manufar kare rayuka da dukiyoyi cikin tasiri. Haka ma Arewa na bukatar sake fasalta ACF daga kungiyar manyan mutane zuwa wata kafa ta jama’a da ke wakiltar muradun manoma, ‘yan kasuwa, dalibai, mata, kwararru, da matasa.

Domin dawo da martaba da kwanciyar hankali, ya zama dole a kafa kwamitin sulhu da garambawul mai zaman kansa, wanda zai kunshi tsofaffin alkalai, dattawa masu kima, sarakunan gargajiya, malamai, kungiyoyin fararen hula, da kwararrun Arewa marasa bangaranci. Wannan kwamiti zai:

Advertisement

Duba kundin tsarin mulkin ACF gaba daya domin ya zama mai wakiltar kowa,

Binciken duk zarge zargen badakala ta kudi,

Advertisement

Samar da hanyoyin tabbatar da gaskiya da rikon amana,

Fayyana iyakokin iko tsakanin bangarorin kungiyar,

Advertisement

Da kuma bayar da shawarwarin da za su bude kofar shiga ga jama’a da dama.

Domin tabbatar da zaman lafiya da sake gina kungiyar, akwai bukatar shugabannin NEC da Kwamitin Aminttattu na yanzu su sauka na wani lokaci domin bai wa tsarin rikon kwarya mai zaman kansa dama. Bayan haka a gudanar da sahihin zabe tare da tuntubar jihohin Arewa baki daya, tare da bai wa matasa muhimmiyar rawa. Tsarin membobinsu ma ya kamata ya zama mai bude kofa ga jama’a maimakon takaita shi ga wasu tsirarun masu fada aji.

Advertisement

Idan kuma bincike ya tabbatar da wawure ko karkatar da kudade, duk wanda aka samu da laifi ko wane matsayi yake da shi , ya kamata ya mayar da kudaden tare da fuskantar hukuncin da ya dace. Rikon amana da gaskiya su ne kadai za su iya dawo wa ACF da martabar da za ta ba ta damar magana da sunan Arewa.

Abu mafi muhimmanci shi ne shugabannin Arewa su fahimci cewa wannan rikici ya wuce rikicin mutane ko mukamai. Babbar matsalar ita ce kara yawaitar gibin da ke tsakanin kungiyoyin shugabanci da talakawan Arewa da ke fama da rashin tsaro, rashin aikin yi, talauci, jahilci, da takaicin rayuwa. Kungiyar da aka kafa domin hada kan Arewa ba za ta iya cigaba da rugujewa saboda rikicin neman iko da anfani kai tsaye ba.

Advertisement

Saboda haka, lokaci ya yi da za a ja layi, a dakatar da rikicin bangaranci, a yi wa kungiyar garambawul cikin jarumta, sannan a gina sabuwar hangen nesa da za ta yi wa talakawan Arewa aiki na gaskiya maimakon kare muradun wasu mutane.

Abbas Ibrahim na rubutu daga Kano, kuma ana iya tuntubarsa ta adireshin email: abbasibrahim664@gmail.com.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending