News
Jami’an DSS Sun Cafke Mutum 5 Ciki Har da ‘Yan Kasar Waje Kan Zargin Sace Ɗalibai A Neja
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta yi nasarar cafke wasu mutum biyar, ciki har da wasu ’yan ƙasar Nijar biyu, bisa zargin hannu a safarar makamai ga ’yan bindigar da suka kai hari makarantar St. Mary’s Catholic School da ke ƙauyen Papiri a Jihar Neja, inda aka yi garkuwa da ɗaruruwan ɗalibai da ma’aikatan makarantar a shekarar da ta gabata.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a wasu samame daban-daban da jami’an DSS suka gudanar a jihohi da dama, yayin da aka kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-103 guda 15, mujallu 15 da harsasai 1,434 na nau’in 7.62mm.
Jami’an DSS Sun Cafke Mutum 5 Ciki Har da ‘Yan Kasar Waje Kan Sace Daliban Papiri A Neja
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun fara cafke Yusuf Mohammed, wanda aka fi sani da Bature, tare da Mubarak Ibrahim a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kaduna yayin da suke kan hanyarsu ta karɓar wasu makamai domin kai wa shugabanninsu.
Majiyoyin tsaron sun ƙara da cewa Yusuf Mohammed na daga cikin mutanen da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo bisa zargin alaƙa da ƙungiyar Boko Haram.
Binciken da aka zurfafa ya kai ga kama Goni Ibrahim, wanda ake zargi da kasancewa babban mai safarar makamai daga yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar. An cafke shi tare da wani abokinsa mai suna Tukur Sani a cikin wata mota mai launin shuɗi.
Bayan waɗannan kamen, jami’an DSS sun sake cafke Alhaji Adamu, wanda aka fi sani da Gado Banufe, a garin Yauri da ke Jihar Kebbi. Ana zarginsa da samar da makamai ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka a Kebbi da sauran jihohin da ke makwabtaka da ita.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa binciken farko ya nuna mutanen biyar da aka kama na daga cikin wata ƙungiyar safarar makamai da ke tallafa wa ’yan bindigar da suka kai harin makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri a watan Nuwamban 2025.
A ranar 21 ga Nuwamban 2025 ne ɗaruruwan ’yan bindiga ɗauke da manyan makamai suka mamaye makarantar kwana ta St. Mary’s Catholic Primary da Secondary School, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da malamai.
Ko da yake kusan ɗalibai 50 sun samu tserewa yayin harin, sama da mutum 250 aka tilasta musu shiga dajin Kainji Lake Reserve.
Sai dai bayan fiye da wata guda da suka shafe a hannun masu garkuwa da mutane, Gwamnatin Tarayya tare da Gwamnatin Jihar Neja sun sanar da ceto tare da dawo da mutum 130 cikin ƙoshin lafiya a ranar 21 ga Disamban 2025.
Hukumomin tsaro sun ce bincike na ci gaba da gudana domin kamo sauran waɗanda ake zargi da hannu a harin da kuma rusa hanyoyin safarar makaman da ke taimaka wa ƙungiyoyin ’yan bindiga a yankin Arewa ta Tsakiya.
