News
FLASHBACK: ‘Yan IPOB Ba ‘Yan Ta’adda Ba Ne, Ina Rayuwa Tare Da Su — Peter Obi
Tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC 2027 Peter Obi, ya taɓa bayyana cewa bai yarda da matakin gwamnatin tarayya na ayyana ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba.
Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Channels Television a shirin Politics Today ranar 1 ga Oktoban 2017, lokacin da yake mamba a Jam’iyyar PDP.
Yankuna 178 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Kano – NEMA
Wani bidiyo na tsohuwar hirar da ke yawo a kafafen sada zumunta ya sake jawo hankalin jama’a tare da tayar da muhawara kan matsayinsa game da ƙungiyar IPOB.
IPOB ƙungiya ce da ke neman kafa ƙasar Biafra mai cin gashin kanta daga yankunan Kudu maso Gabas da wasu sassan Kudu maso Kudu na Najeriya. Gwamnatin tarayya ta haramta ƙungiyar a shekarar 2017 tare da ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.
Sai dai Obi ya ce bai amince da wannan matsaya ba, yana mai cewa:
“Abin da ban yarda da shi ba shi ne kiran IPOB ƙungiyar ta’addanci. A ganina ba ‘yan ta’adda ba ne. Mai yiwuwa waɗanda suka yanke wannan hukunci suna da wasu bayanan da ni ban sani ba.”
Tsohon gwamnan ya ce kasancewarsa mazaunin birnin Onitsha ya sa ya san membobin ƙungiyar sosai, yana mai cewa su mutane ne da yake gani a kullum.
“Ina zaune a Onitsha, kuma zan iya tabbatar da cewa ba ‘yan ta’adda ba ne. Mutane ne da nake haɗuwa da su a kullum a kan tituna,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a duk lokacin da ya ga tarukan da membobin IPOB ke gudanarwa a yankinsa, bai taɓa ganin wata barazana ko cin zarafi ga jama’a daga gare su ba.
“Ina rayuwa tare da su kuma ina hulɗa da su. Sau da yawa ina ganin suna gudanar da taruka, amma ban taɓa ganin wata barazana, tsoratarwa ko cin zarafi daga gare su ba,” in ji Obi.
Kalaman na Peter Obi sun sake fitowa fili ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan matsayar gwamnati da ta ‘yan siyasa game da batun IPOB da matsalolin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin
