News
Yadda Tashar Talabijin Mallakin Gwamnatin Kano Ta Zama Cibiyar Sare Bishiyu Da Sayar Da Itace
Wani rahoton bincike da aka gudanar ya bankado zarge-zargen da ke nuna cewa ana ci gaba da sare manyan bishiyoyi a harabar Abubakar Rimi Television (ARTV), tashar talabijin mallakin Gwamnatin Jihar Kano, lamarin da ya jefa mazauna yankunan Hotoro da kewaye cikin damuwa.
Rahoton ya nuna cewa harabar tashar, wadda aka daɗe ana kallonta a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da suka fi yalwar bishiyoyi a birnin Kano, na fuskantar raguwar manyan bishiyoyi masu muhimmanci ga kare muhalli da daidaita yanayin zafi.
TARIHI: Yadda FEDECO Ta Yi Wa Jam’iyyu Biyar Rajista Domin Fafatawa A Zaɓuɓɓukan Jamhuriya Ta Biyu.
Wasu mazauna yankin da ma’aikatan tashar da suka buƙaci a sakaya sunayensu sun yi zargin cewa ana sare bishiyoyin ne tare da fitar da itatuwan domin harkokin kasuwanci.
A cewarsu, an sha ganin manyan motoci suna shiga da fita daga harabar tashar ɗauke da katako, abin da ya ƙara haifar da tambayoyi kan abin da ke faruwa a wurin.
Majiyoyin sun bayyana cewa wasu daga cikin bishiyoyin da aka sare sun kai shekaru tsakanin 25 zuwa 35 suna girma a harabar, yayin da wasu nau’ikan bishiyoyin gargajiya da ake amfani da su wajen magungunan gargajiya suka kusa ɓacewa gaba ɗaya.
Mazauna yankin sun jaddada cewa bishiyoyin ba wai kawai suna ƙara wa muhalli armashi ba ne, suna kuma taimakawa wajen rage tsananin zafin rana da inganta yanayin iska, musamman a lokacin rani.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Kano ke ci gaba da ƙarfafa manufofin kare muhalli da bunƙasa shuka itatuwa domin yaƙi da matsalolin sauyin yanayi da kare albarkatun ƙasa.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mahukuntan ARTV ba su fito da wata sanarwa a hukumance da za ta yi karin haske kan zarge-zargen da ake yi ba.
Batun ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, inda ake kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace idan har an tabbatar da aikata ba daidai ba.
