News
ARTV Ta Musanta Zargin Sare Bishiyoyi, Yayin Da The Historica Nigeria Ta Tsaya Kan Rahotonta
Jaridar ‘The Historica Nigeria’ ta ce tana nan daram kan rahotonta da ya bayyana zargin sare bishiyoyi masu dimbin a harabar Abubakar Rimi Television (ARTV) da ke Kano, duk da martanin da aka alakanta shi da mahukuntan tashar suka fitar suna musanta zarge-zargen tare da cewa rahoton bai ji ta bakin-su-ba kafin wallafa shi.
Cikin sanarwa da ARTV ta fitar, mahukuntan tashar sun bayyana cewa ba a sare bishiyoyi da yawa ba kamar yadda aka ruwaito, illa kaɗan da aka sare domin tabbatar da tsaro.
2027: An Bukaci Obi Da Kwankwaso Su Bayyana Matsayinsu Kan Sukar Sardauna
Sai dai jaridar ta bayyana cewa kafin wallafa rahoton, ta yi kokarin tuntubar jami’an tashar da abin ya shafa domin samun martaninsu, amma hakan bai samu nasara ba duk da kokarin da aka yi fiye da sau daya.
Jaridar ta kuma bayyana cewa wasu jami’ai a cikin tashar, wadanda suka nemi a sakaya sunayensu, sun tabbatar da damuwar da mazauna yankin Hotoro da kewaye suka nuna dangane da sare bishiyoyin da suka dade a harabar tashar.
Rahoton da The Historica Nigeria ta wallafa ya samo asali ne daga korafe-korafen mazauna yankin da wasu ma’aikatan tashar, wadanda suka yi zargin cewa bishiyoyi masu dimbin shekaru an sare su tare da fitar da itatuwan daga harabar tashar a lokuta daban-daban.
Mazauna yankin sun bayyana cewa harabar ARTV ta kasance daya daga cikin wuraren da suke da yawan bishiyoyi a cikin Kano, inda bishiyoyin ke taka muhimmiyar rawa wajen rage zafi, kare muhalli da kuma samar da iska mai kyau ga al’ummomin da ke kewaye.
Wani daga cikin mazauna yankin ya bayyana cewa bishiyoyin da aka sare ba wai kawai suna da muhimmanci wajen kare muhalli ba ne, har ma suna da amfani wajen samar da magungunan gargajiya.
“Da yawa daga cikin bishiyoyin gargajiya da na asali sun bace gaba daya. Yanzu sai dai a samu irinsu a wasu yankunan karkara, wanda baya akwai su cikin harabar ARTV. Muna amfani da wasu daga cikinsu wajen hada magungunan gargajiya, baya ga rawar da suke takawa wajen kare muhalli da rage tsananin zafi a lokacin rani,” in ji shi.
The Historica Nigeria ta ce har yanzu akwai wasu muhimman tambayoyi da ke bukatar amsa daga mahukuntan tashar.
Daga cikin tambayoyin akwai dalilin sare bishiyoyin tun farko, inda aka kai ragowar itatuwan da aka sare, da kuma ko matsalar tsaro kadai za ta iya zama hujjar cire bishiyoyi masu shekaru da dama da ke bayar da gudunmawa wajen kare muhalli.
Jaridar ta kuma lura cewa sanarwar da ARTV ta fitar domin kare kanta ba ta dauke da sunan ko sa hannun wani jami’in gudanarwa na tashar, lamarin da ya ci karo da ka’idojin aikin yada labarai da sadarwa.
A cewar The Historica Nigeria, sanarwar ta zo ne bayan rahoton da aka wallafa ya jawo hankalin jama’a da masu ruwa da tsaki kan lamarin, wanda ya sa aka fara tattaunawa kan abin da ke faruwa a harabar tashar.
Jaridar ta kara da cewa tun kafin wallafa rahoton, an sanar da jami’an Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar Kano kan zarge-zargen, ciki har da kokarin tuntubar Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi domin samun martaninsa.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata hukuma ta gwamnati da ta sanar da fara bincike a hukumance kan zarge-zargen.
Masana muhalli sun dade suna gargadin cewa sare bishiyoyi ba tare da maye gurbinsu ba na kara tsananta matsalolin dumamar yanayi, karuwar zafi, gurbacewar iska da sauran matsalolin muhalli, musamman a manyan birane irin Kano.
Yayin da mahukuntan ARTV ke ci gaba da musanta zarge-zargen, The Historica Nigeria ta ce tana tsaye kan rahotonta tare da kira ga hukumomin da abin ya shafa, kungiyoyin kare muhalli da kwararru su gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma kare muhalli daga duk wani abu da zai iya haddasa illa ga al’umma nan gaba.
Rahoton ya kuma sake jaddada bukatar dukkan cibiyoyin gwamnati su kasance abin koyi wajen bin dokokin kare muhalli, musamman a dai-dai lokacin da gwamnatin Kano ke kara kaimi wajen yaki da sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba da kuma inganta manufofin kare muhalli a fadin jihar.
