Connect with us

News

Rashin Halartar Kotu Ya Jawo Tsare Sowore A Gidan Gyaran Hali

Published

on

1782127288390

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a tsare ɗan siyasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, a gidan gyaran hali na Kuje har sai an saurari wata buƙata da sabon lauyansa ya gabatar a gaban kotun.

Mai shari’a Muhammad Umar ne ya bayar da umarnin a zaman kotun da aka yi ranar Litinin, bayan da aka gabatar da roƙon neman soke umarnin da kotun ta bayar a baya na janye belin Sowore.

Advertisement

Keir Starmer Ya Yi Murabus Daga Mukamin Firaministan Birtaniya

Tun da farko, a zaman da ya gabata, Sowore bai halarci kotun ba, abin da ya sa masu gabatar da ƙara suka nemi a janye belinsa, suna masu zargin cewa yana ƙoƙarin jan lokaci da kuma kawo cikas ga ci gaban shari’ar.

Advertisement

Rahotanni sun ce ko da yake Sowore ya aika wa kotun wasiƙar neman a dage sauraron shari’ar, bai bayyana dalilin da ya hana shi halartar zaman ba.

Saboda haka, kotun ta yanke shawarar ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da za ta saurari tare da yanke hukunci kan buƙatar da sabon lauyansa ya gabatar.

Advertisement

Ana sa ran shari’ar za ta ci gaba a wani zama na gaba da kotun za ta sanar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending