News
Mazauna Dorayi Sun Ƙalubalanci Shirin Buɗe Film House A Cikin Unguwa, Sun Miƙa Ƙorafi Ga Hukumomi
DAGA HAJARA SANI ABDULLAHI
Al’ummar Dorayi Ƙarama da kewaye a Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano sun miƙa ƙorafi ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano kan shirin buɗe wani Film House a tsakiyar unguwar, inda suka buƙaci a dakatar da aikin har sai an tabbatar da an bi dukkan ƙa’idoji da dokokin da suka dace.
Ƙorafin, wanda aka fitar a ranar 23 ga Yuni, 2026, ya samu goyon bayan wasu ƙungiyoyin al’umma da suka haɗa da Centre for Community Support and Human Development (CCSHD), Gidauniyar Mata Musulmi ta Kano, Community Build and Raise Initiative Hub, Arewa Mu Tashi Mu Farka da Danfodiyo Islamic Center, tare da haɗin gwiwar dattawa, limamai, masu gidaje da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 A Kebbi
A cikin ƙorafin, al’ummar sun bayyana damuwarsu kan yiwuwar tasirin aikin ga tsaro, zaman lafiyar mazauna da kuma tarbiyyar matasa, musamman idan aka yi la’akari da irin ƙalubalen tsaro da yankin ya fuskanta a lokutan baya.
Sun ce, bisa tanade-tanaden dokokin Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da sauran ƙa’idojin zamantakewa, wajibi ne a tabbatar da cewa irin wannan aiki ya dace da tsarin muhalli, al’adun yankin da kuma muradun mazauna kafin a fara aiwatar da shi.
Masu ƙorafin sun jaddada cewa ba sa adawa da ci gaba ko ayyukan da za su amfani jama’a, amma sun buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da an bi doka da ƙa’ida kafin ci gaba da aikin.
Haka kuma, sun yi kira ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, KNUPDA da sauran hukumomin gwamnati da su dakatar da aikin na wucin gadi har sai an kammala tantance dukkan batutuwan da suka shafi amincin al’umma da kuma bin dokokin da suka dace.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Mazauna Dorayi sun aika kwafin ƙorafin zuwa ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Hukumar DSS, Hukumar Hisbah, Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Majalisar Malamai, Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Hakimin Yanki, masu unguwanni da shugabannin masallatai da ƙungiyoyin al’umma domin sanarwa da ɗaukar matakin da ya dace.
Al’ummar Dorayi sun ce za su ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen tabbatar da zaman lafiya, bin doka da oda da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa, tare da kare kyawawan ɗabi’u da al’adun al’umma.
