Connect with us

News

Amurka Da Iran Sun Amince Su Dakatar Da Hare-hare Don Cigaba Da Tattaunawa

Published

on

9d72ca 9978c1ed2eb5422f868d15d604cb57e1mv2 750x536
Advertisements
ads

Amurka da Iran sun amince su dakatar da hare-hare akan juna lamarin da ya gurgunta yarjejeniyarsu ta wucin-gadi, yayin da bangarorin ke shirin komawa tattaunawar da zummar kawo karshen yaƙin Gabas Ta Tsakiya.

Waɗannan hare-hare da suka kai akan junansu sun fito da raunin yarjejeniyar da Pakistan ta shiga tsakani aka cimma don kawo ƙarshen rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da kawo cikas ga jigilar mai ta mashigin ruwa mai muhimmanci na Hormuz.

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Basarake Bisa Zargin Kona Wani Mutum Kan Zargin Satar Itacen Girki

Duk da cewa an tsagaita wuta tun a watan Afrilu, ana cigaba da samun ɓarkewar tashe-tashen hankula jifa-jifa a yankin Tekun Fasha, inda zirga-zirgar jirage a mashigin ruwan ke zama babban silar rikici a kai a kai.

A cikin wani saƙon imel da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na Faransa a daren Lahadi, wani jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa sun tsara shirin cigaba da tattaunawa akan dukkan sassan yarjejeniyar fahimtar juna da kasashen biyu suka cimma.

Haka zalika, jami’in ya bayyana cewa ɓangarorin biyu za su dakatar da ɗaukar matakai na soja a halin yanzu, wanda hakan zai ba da damar gudanar da zirga-zirgar jiragen ruwa ba tare da wata matsala ba a sassan mashigin ruwan na Hormuz.

Advertisement

Iran ba ta gaggauta yin tsokaci kan sanarwar ta Amurka ba, sannan jami’in na Amurka bai tabbatar da rahoton kafofin yada labaran Amurka na cewa za a cigaba da tattaunawar a ranar Talata a kasar Qatar ba.

 

 

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending