Connect with us

News

Indai Dakarun Soji Da Yansanda Sun Kasa, Yansandan Jahohi Ma Ba Abunda Zasu Iya —Buba Galadima

Published

on

Buba Galadima
Advertisements
ads

Jigo a siyasar Najeriya, Buba Galadima, ya bayyana cewa kafa rundunar ‘yan sandan jihohi (State Police) ba zai zama mafita ga matsalar rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta ba.

Galadima ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da ARISE News, inda ya ce idan hukumomin tsaro na ƙasa da suka haɗa da sojoji da rundunar ‘yan sanda ba su iya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro ba, to kafa wata sabuwar rundunar ‘yan sanda a matakin jihohi ba zai sauya lamarin ba.

CVR: Dalilin Da Ya Sanya Kano Ta Zamanto Kan Gaba A Rajistar Katin Zaɓe Yayin Da Kwana 10 Kacal Suka Rage

Ya ce matsalar rashin tsaro da ake fama da ita ta fi ƙarfin ƙara yawan hukumomin tsaro kawai, yana mai nuni da cewa abin da ake buƙata shi ne inganta tsarin tsaro, samar da kayan aiki na zamani da kuma ɗaukar matakan da suka dace wajen yaƙi da masu aikata laifuka.

Galadima ya kuma yi gargaɗin cewa kafa State Police na iya haifar da barazana ga dimokuraɗiyya idan ba a tsara ta yadda ya kamata ba.

A cewarsa, akwai yiwuwar wasu gwamnoni ko masu riƙe da madafun iko su yi amfani da rundunar wajen takura wa abokan hamayya da murƙushe masu adawa da su a siyasance.

Advertisement

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a faɗin ƙasar kan ko kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen rage matsalolin rashin tsaro da suka addabi sassa daban-daban na Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending