News
Ruwan Sama: Jihohi Sama Da 30 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya — Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi al’ummomin da ke zaune a jihohi sama da 30 da Babban Birnin Tarayya (FCT) kan yiwuwar fuskantar ambaliya, sakamakon mamakon ruwan sama da ake hasashen zai sauka tsakanin ranar 22 ga Yuni zuwa 5 ga Yulin 2026.
Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ce ta fitar da wannan gargaɗi a cikin wata sanarwa, inda ta bayyana cewa yankunan da ke bakin koguna, gaɓar ruwa, ƙananan wurare da kuma waɗanda ba su da ingantattun magudanan ruwa ne suka fi fuskantar barazanar ambaliyar.
Ruwan Sama: Jihohi Sama Da 30 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya — Gwamnatin Tarayya
Daga cikin manyan biranen da aka bayyana cewa na iya fuskantar ambaliyar akwai Legas, Abuja, Fatakwal, Ibadan, Lokoja, Makurdi, Benin, Enugu, Owerri da Jos.
Har ila yau, ma’aikatar ta nuna cewa Jihar Adamawa na daga cikin jihohin da ke cikin babban haɗari, inda ta ce al’ummomin Yola, Numan, Mubi, Song da wasu yankuna na iya fuskantar mummunar ambaliya idan ruwan sama ya ci gaba da ƙaruwa kamar yadda aka yi hasashe.
A saboda haka, gwamnatin ta buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa su ɗauki matakan kariya, ciki har da share magudanan ruwa, sa ido kan matakan ruwa a koguna, tanadar hanyoyin neman agajin gaggawa da kuma gujewa zama ko gudanar da harkoki a wuraren da ambaliya ke yawan mamayewa.
Hakazalika, ta yi kira ga gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi da hukumomin agajin gaggawa da su ƙara wayar da kan jama’a tare da shirya matakan ko-ta-kwana domin rage asarar rayuka da dukiyoyi da ambaliya ka iya haifarwa.
