Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya A Nasarawa

Published

on

Screenshot 20240424 191145 (1)

Ɗalibai guda uku na Jami’ar Gwamnatin Tarayya ne aka ruwaito cewa ƴan bandiga sun sace su a jihar Nasarawa, duk da cewa jami’an rundunar ƴan sanda sun samu nasarar ceto guda ɗaya a yayin bincikensu, sai dai har yanzu ba a kai ga samun nasarar ceto sauran mutane biyun ba.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda reshen jihar, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Laraba cikin wata sanarwa da ya fitar.

Guguwar Iska Mai Karfi Ta Hallaka Mutum 7, Yayin Da Fiye Da Mutum 5,400 Ke Cikin Mawuyacin Hali A Jigawa ‎

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa lamarin sace ɗaliban ya faru ne a daren ranar Talata, a ɗakin kwanan ɗalibai da ke wani yanki a bayan gari nesa da wurin da gidajen mazauna jami’ar su ke a birnin Lafia.

Rundunar ta kuma shaida cewa ta samu kiran gaggawa ne a daren daga shugaban jami’an tsaron jami’ar, inda ya sanar mata da cewa wasu ƴan bindiga sun dirarwa gidan kwanan ɗaliban tare da sace mutane uku.

Wanda a dalilin haka nan da nan kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Shettima Jauro Mohammed ya bayar da umarnin gaggawa na tashin tawagar jami’an rundunar don kai ɗauki.

Advertisement

Kakakin rundunar ƴan sandar ya bayyana cewa shirin da su ka yi ya basu damar samun nasarar ceto ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace, wanda kuma har zuwa yanzu suna kan ƙoƙorinsu don ceto ragowar ɗaliban.

A ƙarshe rundunar ta buƙaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da sanya idanu, da kuma buƙatarsu su bayar da haɗin kai ga hukumomin tsaro don taimaka musu wajen ceto sauran ɗaliban.

 

CHANNELSTV

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending