Opinion
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
Daga Abba Anwar
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a Babban Taron Tsaro na Arewacin Najeriya da aka gudanar a Jihar Kaduna. Halartar Garo din ta yi nuni da abubuwa masu muhimmanci.
Masu nazari kan harkokin tsaro sun bayyana cewa zaɓin Garo ya wakilci gwamnan ya dace, duba da irin rawar da ya taka wajen bunƙasa zaman lafiya da inganta tsaro a lokacin da yake Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Masarautu a gwamnatin da ta gabata.
An Kama Wani Mutum Bisa Zargin Fataucin Jaririn Gwaggon biri A Kano
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Yusuf ya yanke shawarar tura mataimakinsa ne saboda gogewarsa da kuma gudummawar da ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar kafin gwamnatin mai ci ta hau mulki a shekarar 2023.
A wancan lokaci, gwamnatin jihar ta ɗora wa Garo nauyin jagorantar shirye-shiryen samar da zaman lafiya tare da yaƙi da matsalolin tsaro a matakin ƙananan hukumomi. Lokacin da aka gudanar da tarukan tsaro a shiyyoyin Sanatoci uku tare da haɗin gwiwar shugabannin ƙananan hukumomi da hukumomin tsaro.
Waɗanda suka shiga cikin wannan shiri sun san irin gudummawar da Garo ya bayar wajen samar da tsaro da haɗa kan masu ruwa da tsaki, lamarin da ya taimaka wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar a lokacin.
Abin farin ciki ne ganin yadda Mataimakin Gwamnan na cikin wakilan gwamnoni a taron tsaron Arewa, wanda aka tattauna batun kafa Asusun Tallafa wa Tsaron Arewacin Najeriya (Northern Nigeria Security Trust Fund). An tsara cewa kowace jiha za ta rika bayar da gudummawar Naira Biliyan Daya (N1b) duk wata domin tallafa wa ayyukan tsaro.
Taron ya gudana ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, inda aka tattauna hanyoyin da za a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya wajen yaƙi da matsalolin tsaro.
Tabbas matakin da Gwamna Yusuf ya ɗauka na tura mataimakinsa ya nuna irin amincewa da yake da shi gare shi, tare da nuna muhimmancin aiki tare domin cimma buri ɗaya.
Lokacin gwamnatin da ta gabata, Garo ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa hanyar samar da tsaron al’umma (Community Policing). Wanda ya taimaka wajen rage matsalolin tsaro a sassa daban-daban na jihar ta hanyoyin kananan hukumomin jihar 44.
Idan har aka aiwatar da Asusun Tallafa wa Tsaron Arewa yadda ya kamata tare da cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya, hakan zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewa.
Gwamna Yahaya ya bayyana a taron cewa matsalolin ‘yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran laifuffuka na ci gaba da kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Arewa.
Amma dama ba tun yau ba gwamnatin Kano karkashin Gwamna Yusuf ta fara ɗaukar matakai da suka dace wajen ƙarfafa tsaro da yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Misali an kafa rundunar Neighborhood Watch Guards, wadda aka tura cikin al’ummomi domin taimakawa hukumomin tsaro wajen rage laifuffuka irin su sace-sace a cikin gidaje da kuma ƙwacen wayoyin hannu.
Haka kuma, kwanaki kaɗan kafin taron tsaron Arewa, Gwamna Yusuf ya sanar da kafa Kwamitin Musamman Mai Ƙarfin Iko Kan Yaƙi Da Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi. Tsarin jagorancinsa ya nuna jajircewar ƙudurin gwamnati na magance matsalar.
Waɗannan matakai sun nuna cewa Jihar Kano ta fara aiwatar da manufofin da suka yi daidai da manufar Babban Taron Tsaro na Arewacin Najeriya din. Ba abinda za mu ce sai fatan Allah Ya taimaki gwamnoninmu wajen kare wadannan matsaloli.
Kuma wakilcin da Mataimakin Gwamna Garo ya yi a taron ya tabbatar da irin jajircewar gwamnatin Kano wajen samar da zaman lafiya. Idan ba a manta ba Garo na daga cikin waɗanda suka taka rawa wajen inganta tsaro a jihar a shekarun baya. Musamman ta hanyar shigar da kananan hukumomin mu ka’in- na’in.
Shi Maigirma Garo, wanda Gwamna Yusuf ya taɓa bayyanawa a matsayin “mataimaki mai biyayya”, ya kasance mutum mai kishin samar da ingantaccen tsaro ga Kano da Arewacin Najeriya baki ɗaya.
Abba Anwar ya rubuto wannan daga Kano
Asabar, 11 ga Yuli, 2026
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News5 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
