Connect with us

News

Kano: Gini Ya Rufta Kan Dalibai A Makarantar Islamiyya

Published

on

IMG 20260815 174132 662

Wani gini ya rufta a makarantar Khadija Bala Idris ta Hafizul Qur’an da ke Kurna Kwachiri, a Jihar Kano, yayin da dalibai suka shiga wani aji domin cin abinci kafin fara karatunsu.

Shugaban makarantar ya tabbatar wa Jaridar Inda Ranka faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar, yayin da ake ruwan sama a yankin.

Gini Ya Rufta Kan Uwa Da ’Ya’yanta 2 AKaduna

A cewar bayanan da aka samu, daliban sun shiga ajin ne domin cin abinci kafin fara karatun, sai ginin ya rufta ba zato ba tsammani.

Bayan faruwar lamarin, aka fara aikin ceto domin kubutar da daliban da ka iya makalewa karkashin baraguzan ginin, kuma an garzaya da Ɗalibai  8 su zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Kawo yanzu, ba a samu cikakken bayani kan adadin wadanda suka jikkata ko kuma ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending