News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 3 Kan Zargin Satar Taransfoma A Neja
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta sanar da cafke wasu mutane tara da ake zargi da hannu wajen fasa shaguna, satar kayayyaki, karɓar kayan sata da kuma satar manyan taransfoma guda biyu masu ƙarfin 1000KVA.
Rundunar ta bayyana cewa ta kwato wasu kayayyakin gyaran motoci da aka sace, waɗanda darajarsu ta kai kimanin Naira 600,000. Haka kuma, an kama wani mutum da ake zargi da safarar ɗaya daga cikin taransfoman da aka sace daga gidan wutar lantarki na Federal Housing Estate da ke yankin Tungan Shanu.
Watan Maulidi Lokaci Ne Na Yawaita Ibada Da Ayyukan Alheri – Dr Yunusa
Binciken farko da jami’an tsaro suka gudanar ya nuna cewa ana zargin an sayar da kowanne daga cikin taransfoman da aka sace kan kudi Naira 750,000.
Rundunar ’yan sandan ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da wasu mutane biyu da har yanzu ake nema ruwa a jallo.
Ta ƙara da cewa waɗanda aka kama suna hannun jami’an tsaro domin kammala bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar tuhuma bisa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News5 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News3 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
