Connect with us

News

2027: Daraktocin RBDAs Sun Kafa Kungiya Don Tattara Kuri’un Manoma Miliyan 20 Ga Shugaba Tinubu

Published

on

Yayin da babban zaben 2027 ke kara matsowa, wasu Daraktocin Gudanarwa na hukumomin raya koguna da mada tsan-ruwa (River Basin Development Authorities) sun kafa wata kungiya da ta ce za ta yi kokarin samun kuri’un manoma sama da miliyan 20 domin bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu goyon baya a zaben.

Kungiyar ta kunshi manyan jami’an hukumomin River Basin daga yankuna daban-daban na Najeriya, inda ta ce za ta mayar da hankali wajen bayyana wa manoma ayyukan da gwamnatin tarayya ta aiwatar a bangaren noma.

APC Ta Musanta Janye Jerin Sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen 2027

An zabi Dahiru Hammandilko, Daraktan Ayyukan Noma na Upper Benue River Basin Development Authority (UBRBDA), a matsayin shugaban kungiyar.

Musa Illiyasu Kwankwaso, Daraktan Kudi na Hadejia-Jama’are River Basin Development Authority, shi ne babban jami’in dabarun kungiyar, yayin da Sowede Oluwalayode, Daraktan Injiniya na Ogun-Osun River Basin Development Authority, ya zama sakataren kungiyar.

Sauran jami’an kungiyar sun hada da Dr Abubakar A. Kudi, Daraktan Tsare-tsare da Zane na yankin Arewa ta Tsakiya, wanda aka nada a matsayin sakataren kudi; Asadu Evaristus daga Anambra-Imo River Basin Development Authority, wanda ya zama sakataren shirye-shirye; da Felix Kurogha, Daraktan Ayyukan Noma na Niger Delta Basin Development Authority, wanda aka nada a matsayin sakataren yada labarai.

Advertisement

Da yake magana kan kafa kungiyar, Kwankwaso ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar da shirye-shirye da dama da nufin sauya fasalin harkar noma da tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.

Ya ce jami’an River Basin na da muhimmiyar rawa wajen tallafa wa manoma, musamman ta fuskar samar da ruwa domin noman rani, saboda haka suna cikin wadanda suka fi sanin irin tasirin shirye-shiryen gwamnatin a fannin noma.

«“Mu da muke tsakiyar harkar noma, musamman saboda rawar da muke takawa wajen samar da ruwa ga manoma, mu ne ya kamata mu bayyana abin da Shugaba Tinubu ya yi a cikin shekaru uku da suka gabata,” in ji shi.»

Kwankwaso ya ce manoma da dama sun amfana da shirye-shiryen gwamnatin tarayya, lamarin da ya taimaka wajen saukaka ayyukan noma da kara yawan amfanin gona.

Ya kuma yi ikirarin cewa karin samar da abinci ya taimaka wajen rage farashin wasu kayayyakin amfanin gona a kasuwanni.

A cewarsa, farashin buhun shinkafa wanda a baya ya haura N100,000, yanzu ya ragu zuwa  N50,000.

Advertisement

“Wannan sauyin ba zai yiwu ba idan ba don matakan da gwamnati ta dauka ba,” in ji shi.

Daraktan ya ce kungiyar za ta yi aiki tare domin ganin manoma sama da miliyan 20 da suka ci gajiyar shirye-shiryen gwamnatin tarayya sun goyi bayan Tinubu a zaben 2027.

Ya ce gwamnatin tarayya ta kuma samar da taki tare da rarraba shi ga miliyoyin manoma ta hannun gwamnatocin jihohi, yana mai cewa taki na daga cikin muhimman abubuwan da ke taimakawa wajen samar da abinci.

Kwankwaso ya kawo misalin Kano, inda ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samar da takin zamani mai yawa tare da rarraba shi ga manoma kan farashi mai rahusa.

Ya ce irin wadannan matakai na faruwa a sassa daban-daban na kasar, yana mai cewa hakan ya sa manoma ke shirin nuna goyon bayansu ga Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, da sauran ‘yan takarar APC a zaben 2027.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending