News
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
Rundunar Tsaron Farar Hula da Tsaron Kasa (NSCDC) ta Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargin suna satar shanu, dauke da wata saniya da ake zargin sata ce a Karamar Hukumar Kiru.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026.
Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 Ga Satumba A Matsayin Ranar Hutun Bikin Takutaha
Ya ce jami’an rundunar sun kama mutanen ne yayin da suke bakin aiki a wani shingen bincike da ke Tudunwada Rahama Rawun da ke Karamar Hukumar Kiru.
A cewarsa, jami’an sun cafke wadanda ake zargin ne da tsakar dare, yayin da suke dauke da saniyar da ake zargin an sace.
SC Ibrahim ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma gano asalin saniyar.
Ya kara da cewa, bayan kammala bincike, rundunar za ta dauki matakin da ya dace kan wadanda ake zargin, kamar yadda doka ta tanada.
