Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Kwalara A Wasu Sassan Jihar

Published

on

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kano (KNCDC) ta tabbatar da bullar cutar kwalara a wasu sassan jihar, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 227.

Babban Daraktan hukumar, Farfesa Muhammad Adamu Abbas, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano a wannan makon.

Sauron Da Jirgi Ya Dauko Daga Afirka Sun Yi Ajalin Mutane 2 A Jamus

Ya ce bayan hukumar ta samu rahoton bullar cutar, ta gudanar da bincike tare da tabbatar da kamuwa da cutar, inda aka bai wa wadanda suka kamu kulawar da ta dace.

A cewar daraktan, daga cikin mutane 227 da aka tabbatar sun kamu, 15 ne ke bukatar kulawa ta musamman, yayin da sauran ke ci gaba da samun kulawar lafiya da ta dace.

Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su gaggauta kai duk wanda ya fara nuna alamomin amai da gudawa zuwa asibiti domin samun kulawa cikin gaggawa da kuma rage yiwuwar kara yaduwar cutar.

Advertisement

KNCDC ta ce daukar matakin gaggawa da neman magani da wuri na da muhimmanci wajen dakile yaduwar kwalara a tsakanin al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending