Connect with us

News

Mutum 1,000 Sun Kamu Da Cutar Mashako A  Katsina

Published

on

Zazzabin Lassa Cutar ta yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku

Akalla mutane 1,000 ne suka kamu da cutar mashako a ƙananan hukumomi 26 na Jihar Katsina cikin watanni takwas da suka gabata.

Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta jihar, Dakta Shehu Kabir, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai kan halin da cutar ke ciki a jihar.

Messi Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Argentina Ƙwallo

Ya ce akwai alamun cewa kusan kashi biyar cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar sun rasa rayukansu, sai dai ya ce wannan adadi na buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da sahihancinsa.

Dakta Kabir ya ce ƙananan hukumomin Funtua, Kankiya, Bakori, Katsina, Mashi da Daura na daga cikin wuraren da aka fi samun masu fama da cutar.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar, ciki har da gudanar da allurar rigakafi a ƙananan hukumomin Bakori, Charanchi, Funtua, Mashi da Kankiya.

Advertisement

A cewarsa, an kuma kafa cibiyoyin kula da masu fama da cutar guda uku a biranen Katsina, Funtua da Daura, domin ba da kulawar gaggawa ga waɗanda suka kamu da ita.

“Gwamnati ta kuma samar wa jami’an lafiya magungunan da ake buƙata domin kula da masu fama da cutar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an horas da jami’an lafiya kan hanyoyin sa ido, gano masu kamuwa da cutar, ɗaukar matakan gaggawa da kai rahoton bullar cutar domin a samar da kulawa cikin lokaci.

Cutar mashako na iya haifar da matsalar numfashi, bushewar makogaro da zazzabi.

Dakta Kabir ya yi kira ga hakimai, dagatai da masu unguwanni da su taimaka wa jami’an lafiya wajen wayar da kan al’umma, musamman iyaye, kan muhimmancin kai yara wuraren da ake gudanar da allurar rigakafin cutar..

 

Advertisement

 

CHANNELSTV

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending