Connect with us

News

EFCC Ta Kori Ma’aikata Fiye Da 40 Kan Cin Hanci Da Rashawa

Published

on

Hukumar EFCC Ta Kori Jami’anta 27 Bisa Laifin Zamba Da Rashin Da

Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ce ta kori sama da ma’aikatanta 40 cikin shekaru uku da suka gabata bisa zargin cin hanci da rashawa da kuma badakalar kuɗi.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a hedikwatar EFCC da ke Abuja, yayin wani taron manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu tun bayan da ya karɓi ragamar shugabancinta.

Olukoyede ya ce cikin shekaru biyu da rabi zuwa uku da ya yi a matsayin shugaban hukumar, ya bayar da umarnin korar ma’aikata sama da 40 da aka samu da hannu wajen aikata cin hanci da rashawa ko badakalar kuɗi.

Ya kuma bayyana cewa sama da biyar daga cikin ma’aikatan da aka kora ana gurfanar da su a gaban kotu, yayin da ake kammala shirye-shiryen gurfanar da wasu.

“A cikin shekaru biyu da rabi zuwa uku da na yi a nan, na nemi a kori sama da ma’aikata 40 saboda cin hanci da rashawa da kuma badakalar kuɗi. Sama da biyar daga cikinsu ana gurfanar da su a yanzu,” in ji shi.

Shugaban EFCC ya ce hukumar ba za ta iya gurfanar da mutanen da ke aikata laifukan cin hanci da rashawa ba, sannan ta yi wa ma’aikatanta sassauci idan sun aikata irin waɗannan laifuka.

Advertisement

Ya ce wasu daga cikin shari’o’in ma’aikatan suna gaban kotu, yayin da ake shirya takardun gurfanar da wasu.

Haka kuma, Olukoyede ya bayyana cewa hukumar ta sauya sunan tsohon sashen kula da harkokin cikin gida zuwa Sashen Da’a da Mutunci, domin ƙara tabbatar da tsaftar cikin hukumar.

Ya ce EFCC ta kuma samar da wata manufar kula da kyaututtukan da ma’aikata ke karɓa, domin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana.

A cewarsa, ma’aikatan za su bayyana kadarori ko kyaututtukan da suka karɓa idan darajarsu ta haura wani ƙayyadadden matsayi, ciki har da kyaututtukan da ‘yan uwansu da ke ƙasashen waje suka turo musu.

Ya ce manufar za ta taimaka wajen tabbatar da cewa ma’aikatan hukumar za su iya bayyana tushen dukiyarsu da kuma yadda suke samun abin gudanar da rayuwarsu.

“Dole ne ku tabbatar hannuwanku suna da tsabta. Ba za ku iya yaƙar cin hanci da rashawa ba alhali hannuwanku sun gurɓata da ayyukan cin hanci,” in ji Olukoyede.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending