News
NUJ Kano Ta Yi Allah-wadai Da Harin Da Aka Kai Wa ’Yan Jarida
Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kano, ta yi kakkausar suka tare da yin Allah-wadai da harin da aka kai wa wasu ’yan jarida da ke aikin ɗaukar rahoto kan taron siyasar APC a Kano.
Harin ya faru ne ranar Asabar bayan kammala wani taron siyasa a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, yayin da ’yan jaridar ke kan hanyarsu ta komawa ofis.
NUJ Kano Ta Yi Allah-wadai Da Harin Da Aka Kai Wa ’Yan Jarida
Rahotanni sun ce wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai wa motar Radio Nigeria, Pyramid FM Kano, hari a bayan City Campus na Jami’ar NorthWest, Kofar Nassarawa, inda suka fasa gilasan motar tare da lalata wasu sassan ta.
A cikin wata sanarwa da Shugaban NUJ na Kano, Kwamared Suleiman Abdullahi Dederi, da Sakatariyar ƙungiyar, Kwamared Hauwa Sani Zaharaddeen, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana harin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.
NUJ ta ce harin barazana ne ga ’yancin aikin jarida, tana mai jaddada cewa bai kamata a tsoratar da ’yan jarida ko musguna musu yayin da suke gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu na sanar da jama’a abin da ke faruwa ba.
An yi amfani da adda da wukake
Ɗaya daga cikin ’yan jaridar Pyramid FM, Yakubu Abubakar Gwagwarwa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa a cikin motar akwai ma’aikatan Pyramid FM guda huɗu, wani ɗan jarida daga Guarantee Radio da kuma ’yan sanda uku da aka ɗauka daga filin taron.
Ya ce maharan sun yi amfani da adda da wukake wajen bugun motar akai-akai, inda suka fasa gilasan motar duk da kasancewar jami’an tsaro a cikinta.
A cewarsa, direban motar ya samu rauni yayin harin, yayin da wasu daga cikin mutanen da ke cikin motar suka ji rauni sakamakon gutsattsarin gilashin da aka fasa.
Gwagwarwa ya ce maharan sun ci gaba da bin motar bayan da suka yi ƙoƙarin juyawa domin tserewa daga wurin.
Sai dai ɗan jaridar ya ce ba ya ganin cewa an kai harin ne kai tsaye saboda aikin jarida, yana mai bayyana lamarin a matsayin wani hari da ka iya zama bazuwar wanda wasu mutane ma za su iya fuskantar irin sa.
NUJ ta nemi bincike
NUJ Kano ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, domin gano wadanda suka aikata harin tare da gurfanar da su a gaban kotu idan aka same su da laifi.
Ƙungiyar ta ce barin irin wannan hari ba tare da ɗaukar matakin da ya dace ba na iya ƙarfafa wasu su sake kai hare-hare kan ’yan jarida a nan gaba.
Ta kuma nuna damuwa kan yadda tsaron ’yan jarida ke ƙara zama abin tambaya yayin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban zaɓen 2027.
NUJ ta yi kira ga jam’iyyun siyasa
Kungiyar ta yi kira ga jam’iyyun siyasa, magoya bayansu da masu shirya tarukan siyasa da su tabbatar da tsaron ’yan jarida a yayin gudanar da ayyukansu.
Ta ce ’yan jarida ba ’yan siyasa ba ne, kuma aikinsu shi ne isar da bayanai ga jama’a cikin gaskiya, adalci da ƙwarewa.
NUJ ta kuma jajanta wa hukumar gudanarwa da ma’aikatan Radio Nigeria, Pyramid FM Kano, bisa barnar da aka yi wa motarsu, tare da nuna goyon bayanta ga ’yan jaridar da suka fuskanci lamarin.
Rahotanni sun ce kawo yanzu rundunar ’yan sandan Kano ba ta fitar da sanarwa kan harin ba.
Kungiyar ta ce za ta ci gaba da tuntubar hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa ’yan jarida a Kano sun samu damar gudanar da aikinsu cikin tsaro da ’yanci.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
