News
Jami’an Ƴansanda Sun Ceto Yara 17 Da Aka Sace A Oyo
Rundunar ’yan sandan jihar Oyo da ke kudancin Najeriya ta ce ta ceto ƙananan yara 17 da aka sace, masu shekaru tsakanin biyu zuwa bakwai.
Rundunar ta ce ta kama mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen satar yaran da safarar su zuwa wasu sassan ƙasar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Oyo, CP Abimbola Ayodeji Olugbenga, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Eleyele, Ibadan.
Ya ce an ceto yaran ne daga maɓoyar waɗanda ake zargin a jihohin Oyo, Ogun da Delta, bayan gudanar da bincike kan satar yaran.
A cewar kwamishinan, ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, wata mata mai suna Adejoke Popoola, ta amsa cewa ta taɓa satar yara sama da 15 a wurare daban-daban.
Ya ce binciken ’yan sandan ya nuna cewa ana satar wasu daga cikin yaran ne a coci-coci da kuma wuraren gudanar da bukukuwa.
A garin Mowe na jihar Ogun, jami’an tsaro sun kama wata mata mai suna Adekanbi Jannet, inda suka ceto yara huɗu tare da wasu mata biyu masu juna biyu.
Haka kuma, a jihar Delta, rundunar ta ce ta ceto wasu yara huɗu daga hannun Christopher Joy, mai shekara 48, da Rosemary Jesse, mai shekara 53. Ana zargin mutanen da karɓar yaran daga Oyo domin sayar da su a Delta.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai Alfa Murtala Fasasi da kuma Yakubu Azeez, wanda rundunar ta bayyana a matsayin boka. ’Yan sandan sun ce ana zargin waɗannan mutane da hannu wajen amfani da sassan jikin yara wajen ayyukan tsafi da neman kuɗi.
