News
Duk Shekara Makarantu Masu Zaman Kansu Za Su Rika Sabunta Lasisinsu — Gwamnatin Kano
Hukumar Kula da Cibiyoyi da Makarantu Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano ta ce daga yanzu dukkan makarantun masu zaman kansu da ke a jihar za su rika sabunta lasisin gudanar da ayyukansu duk shekara.
Babban Sakataren hukumar, Baba Abubakar-Umar, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Kano ranar Talata.
Kotu Ta Daure Mutane Biyu Shekara 9 Kan Bai Wa Yara Abubuwan Maye A Kano
Ya ce kudin sabunta lasisin na shekara-shekara shi ne Naira 6,000.
Baba Abubakar-Umar ya ce hukumar na kuma bukatar makarantun masu zaman kansu su kiyaye ka’idojin ilimi da aka shimfida domin tabbatar da ingancin koyarwa da kuma tsaron dalibai.
Ya bayyana cewa duk wanda ke son kafa sabuwar makaranta dole ne ya gabatar da takardar neman izini, kafin jami’an hukumar su gudanar da bincike kan wurin da kayan aikin makarantar.
Babban Sakataren ya ce kafin a yi wa dokar kwaskwarima, ana sabunta lasisin makarantu ne bayan shekaru uku.
Sai dai ya ce an sauya dokar domin a rika sabunta lasisin duk shekara, a wani bangare na kokarin gwamnatin Kano na inganta harkar ilimi a jihar.
Haka kuma, ya gargadi masu makarantu kan kara kudaden makaranta ba tare da dalili mai inganci ba.
Ya kara da cewa duk wani sauyin kudin makaranta ya kamata ya gudana tare Kungiyar Iyaye da Malamai (PTA) domin samun matsaya da ta dace tsakanin masu makarantu da iyaye.
-
News6 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News5 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News6 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

