News
An Buɗe Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna Da Majalisun Jihohi A Najeriya
A ranar Talata, 8 ga Satumba, aka buɗe ƙofar soma yaƙin neman zaɓen gwamna da ’yan Majalisun Dokokin Jihohi a faɗin Najeriya, bisa jadawalin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar.
A cewar jadawalin INEC na zaɓen 2027, an fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ’yan Majalisar Tarayya tun ranar 19 ga Agusta.
Jihohi 28 ne za su gudanar da zaɓen gwamna, inda ’yan takara za su fara gabatar da manufofinsu ga masu zaɓe ta hanyar taruka, kafafen yaɗa labarai da sauran hanyoyin neman ƙuri’a.
Jam’iyyun APC, NDC da ADC na daga cikin manyan jam’iyyun da suka tsayar da ’yan takarar gwamna a jihohin 28.
Sai dai wasu manyan jam’iyyun har yanzu ba su kammala kafa ko ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓensu ba, duk da fara lokacin yakin neman zaɓen.
Rahotanni sun ce APC na nazarin wasu naɗe-naɗen da ta yi a kwamitin yaƙin neman zaɓenta bayan samun koke-koke kan wasu mambobin kwamitin.
Haka kuma, NDC, ADC da PDP ba su ƙaddamar da wasu daga cikin tsare-tsaren yaƙin neman zaɓensu ba.
Masana siyasa na danganta jinkirin da rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓukan fidda gwani, ƙarancin kuɗi da tattaunawar ƙulla ƙawance gabanin zaɓen.
Aminiya ta ruwaito cewa ba za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Imo, Ondo, Osun, Bayelsa, Edo, Kogi, Ekiti da Anambra ba, saboda jadawalin zaɓensu ya bambanta da na sauran jihohin..
