News
Yan Sanda Sun Kama Wanda Da A Ke Zargi Da Hallaka Budurwarsa A Kaduna
Rundunar ƴan sandan a Kaduna ta kama wani mutum da a ke zargi da hannu a mutuwar budurwarsa Rebecca Jeremiah.
Ƴan sandan sun ce mutumin shi ne na ƙarshe da ya yi magana da marigayiyar kafin daga bisani aka gano gawarta a yankin Romi, cikin ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Mutum Ya Na Kokarin Sayar Da ‘Yarsa Yar Watanni 16
A cewar rundunar lamarin ya faru ne ranar 5 ga Satumba, bayan samun rahoton gano gawar Rebecca a kan titin Mai Angwa da ke Romi. An garzaya da ita zuwa Asibitin St. Gerald da ke Kakuri, inda likita ya tabbatar da rasuwarta.
Rundunar ta ce an kama wanda a ke zargin a wurin aikinsa na kamfanin Tomato Jos da ke Maraban Jos, cikin ƙaramar hukumar Igabi.
A lokacin da a ke yi masa tambayoyi rundunar ta ce wanda a ke zargin ya amsa cewa sun samu saɓani ne a ɗakinsa kan kiran wayar da wata mata ta yi masa. Rundunar ta ce ya bayyana cewa rikicin ya kai ga mutuwar matar sannan ya kai gawarta wani fili kusa da gidansa domin ɓoye laifin.
A halin yanzu, wanda a ke zargin yana hannun ƴan sanda, yayin da a ke ci gaba da bincike. Rundunar ta ce za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.
Kwamishinan ƴan sanda a jihar Rabiu Muhammad ya yi Allah-wadai da duk wani nau’in tashin hankali tare da kira ga jama’a da su riƙa warware saɓanin da ke tsakaninsu cikin lumana.
