News
Matar Da Ta Haifi ‘Yan Biyar Ta Rasa Su Duka Bayan Kwana Uku Da Haihuwa
Wata ’yar kasar Kenya, Mercy Kanini, mai shekaru 28, ta rasa ’ya’yanta biyar da ta haifa lokaci guda, bayan dukkan jariran sun rasu cikin kwanaki uku da haihuwarsu.
Kanini ta haifi ’yan biyar ne a ranar 13 ga Satumba, 2026, inda ta haifi dukkan su ba tare da an yi mata tiyatar haihuwa ba.
Majalisar Tarayya Ta Miƙa Ƙudirin ’Yan Sandan Jihohi Ga Majalisun Jihohi 36
Asibitin Kasa na Kenyatta, babban asibitin kula da marasa lafiya da ke Kenya, ya tabbatar da mutuwar jariri na biyar kuma na ƙarshe a ranar Laraba.
A cewar asibitin, an haifi jariran ne kafin lokacin haihuwa ya cika, kuma suna da ƙarancin nauyi sosai a lokacin haihuwa.
Asibitin ya ce jariran sun fuskanci “manyan ƙalubalen lafiya” sakamakon ƙarancin nauyin da suke da shi, lamarin da ya sa suka kasa tsira duk da kulawar da ake ba su.
Mutuwar jariran ta mayar da farin cikin da iyalin Kanini suka shiga bayan haihuwar ’yan biyar zuwa babban alhini, bayan da ta rasa dukkan ’ya’yanta cikin kwanaki uku kacal.
