Connect with us

News

Sama Da Yankuna 8,000 Da Makarantu 4,500 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa    — Gwamnatin Tarayya 

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

Sama Da Yankuna 8,000 Da Makarantu 4,500 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa

— Gwamnatin Tarayya

 

 

Hukumar kula da albarkatun ruwa ta Najeriya, NiHSA, ta yi gargaɗin cewa sama da Yankuna dubu 8,000 da makarantu 4,500 a jihohi 15 na Najeriya na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa tsakanin ranar 19 zuwa 25 ga watan Satumba.

Hukumar ta ce ƙaruwar ruwan koguna na iya haifar da ambaliyar ruwa a wasu Yankuna da ke cikin haɗari, lamarin da ka iya shafar makarantu, asibitoci, kasuwanni, wuraren ibada da gonaki.

Advertisement

An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja

Gargaɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar hasashen ambaliyar ruwa ta ƙasa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar kuma Babban Jami’in Gudanarwa na hukumar, Arch Umar Mohammed.

Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Imo, Cross River, Delta, Ebonyi, Benue, Anambra, Akwa Ibom, Edo, Enugu, Bayelsa, Kogi, Abia, Taraba, Rivers da Lagos.

NiHSA ta buƙaci gwamnatocin jihohin da abin ya shafa su gaggauta kwashe mazauna yankunan da ke cikin haɗari zuwa wuraren da suka fi aminci, kafin lokacin da aka yi hasashen ambaliyar.

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending