News
Dakarun Soji Sun Samu Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda 36
Hukumar Tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa dakarun sojin kasar sun samu nasarar Hallaka ’yan ta’adda 36 tare da ceto mutane 50 da aka yi garkuwa da su a samamen da suka gudanar a sassan kasar daban-daban.
Daraktan yada labarai na hukumar, Manjo Janar Michael Onoja ne ya tabbatar da cewa dakarun sun kuma kame wasu da ake zargin aikata ta’addanci, tare da kwace dumbin makamai da alburusai da kayayyakin more rayuwa na miyagun.
NDLEA Ta Sake Kama Wata Tsohuwa Mai Shekara 83 Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi
Wannan na ɗaya daga cikin jerin samamen da rundunar ke ci gaba da kaiwa domin kakkabe ayyukan ta’addanci da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasar.
Wannan gagarumar nasara na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke kara kaimi wajen fatattakar kungiyoyin masu garkuwa da mutane da masu tayar da kayar baya domin dawo da cikakken tsaro da kwanciyar hankali ga al’umma.
A yankin Arewa maso Gabas, dakarun sun kashe ‘yan ta’adda 26 tare da daƙile harin da mayakan ISWAP suka yi ƙoƙarin kai wa garin Kukawa da ke Jihar Borno, inda a yankin Kudu maso Gabas kuma aka ceto mutum 20 da ke shirin shiga aikin yi wa ƙasa hidima da aka sace.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, aikin dakarun ya samu nasarar kashe wani babban kwamandan ƙungiyar ISWAP a jihar Ondo da ke Kudu maso Yamma.
