Connect with us

News

Ya kamata masu ikon fada aji su shiga tsakani kan rikicin masarauta a Kano – Kungiyar Friends of Kano

Published

on

images (4)

Ƙungiyar Friends of Kano ta yi kira ga dattawa, malaman addini, ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a Jihar Kano da su shiga tsakani domin kawo ƙarshen takaddamar masarautar Kano da samar da mafita mai ɗorewa.

 

Shugaban ƙungiyar, Comrade Abdullahi Isah, ne ya yi wannan kiran, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda rikicin da ya daɗe yana faruwa ke barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban tattalin arzikin jihar.

 

Ya ce Kano jiha ce da ta shahara wajen kasuwanci da harkokin tattalin arziki, don haka ya zama wajibi masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen magance matsalar kafin ta ƙara ta’azzara.

 

Advertisement

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa takaddamar masarautar na iya yin illa ga harkokin kasuwanci da jawo fargaba tsakanin ’yan kasuwa, inda ta bayyana damuwar cewa wasu daga cikinsu na iya tunanin ƙaura daga jihar sakamakon rashin tabbas kan zaman lafiya.

 

Haka kuma, Friends of Kano ta buƙaci gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta kafa kwamiti mai ƙarfi da zai yi nazari kan rikicin tare da tattaunawa da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa domin samar da mafita ta dindindin.

 

Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin tattaunawa, haƙuri da fahimtar juna wajen warware takaddamar, tana mai cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƙan ci gaban Kano da bunƙasar tattalin arzikinta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending