Connect with us

News

Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

Published

on

IMG 20261016 WA0004

Daga Muhammad Kabir, Kano

Mai magana da yawun Ƙungiyar Masu Riƙe da Muƙaman Siyasa ta Jihar Kano, Dr. Musa Illiyasu Kwankwaso, ya bayyana Sanata Basheer Lado a matsayin gogaggen ɗan siyasa da ya ƙware wajen tafiyar da harkokin siyasa cikin hikima da mutunta juna.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake taya Sanata Lado, Mashawarcin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan Harkokin Majalisar Ƙasa, musamman Majalisar Dattawa, murnar cika shekaru 60 da haihuwa.

Boko Haram, ISWAP Na Ci Gaba Da Barazana Ga Tsaro — Gwamna Fintiri

Sanata Lado, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Masu Riƙe da Muƙaman Siyasa, ya samu yabo daga Kwankwaso bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa dimokuraɗiyya, ayyukan jin ƙai da ci gaban Najeriya.

Kwankwaso ya ce Sanata Lado amintaccen ma’aikacin gwamnati ne kuma gogaggen ɗan majalisa wanda ƙwarewarsa ta taimaka wajen ƙarfafa alaƙar aiki tsakanin bangaren zartarwa da Majalisar Dattawa.

Advertisement

Ya ce, “Sanata Lado mutum ne mai ƙwarewa a harkokin siyasa, wanda yake gudanar da ayyukansa cikin mutunta juna da fahimtar juna.”

Sanata Lado ya wakilci Mazabar Sanatan Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta Bakwai daga shekarar 2011 zuwa 2015, inda ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban kwamitin majalisar mai kula da ayyukan gine-gine da hanyoyi.

A lokacin da yake majalisa, ya taimaka wajen samar da ayyukan raya ƙasa da dama, ciki har da gadar Kundila da aka fi sani da Gadar Lado a Jihar Kano.

Bayan kammala wa’adinsa a majalisa, Sanata Lado ya riƙe wasu muƙaman gwamnati, ciki har da Kwamishinan Tarayya na Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Baƙi da Masu Rasa Muhallansu (NCFRMI), da kuma Darakta-Janar na Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP).

Kwankwaso ya ce Sanata Lado ya bayar da gudunmawa wajen kare haƙƙin masu rauni a cikin al’umma, yaƙi da safarar mutane da inganta walwalar mutanen da rikice-rikice suka raba da muhallansu.

Haka kuma, ya yaba wa gidauniyar Ladon Alheri Foundation bisa ayyukan tallafawa al’umma, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, ƙarfafa tattalin arzikin mata, samar da ruwan sha a ƙauyuka da taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi.

Advertisement

Ya ce ayyukan Sanata Lado a fannoni daban-daban na nuna jajircewarsa wajen hidimtawa al’umma da bayar da gudunmawa ga ci gaban Najeriya.

Kwankwaso ya yi masa fatan ƙarin lafiya, tsawon rai da nasara a sauran ayyukan da yake gudanarwa domin ci gaban ƙasa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending