Connect with us

News

An Kama Likita Da Mahaifiya Kan Zargin Sayar Da Jaririya

Published

on

Jaririi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta kama wani likita da mahaifiyar wata jaririya mai wata ɗaya bisa zargin sayar da jaririyar kan Naira miliyan biyu.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Dakta Adeleke Ebenezer, mamallakin Asibitin Ebepraise da ke garin Ido a jihar, inda aka haifi jaririyar, da mahaifiyarta mai suna Cecilia.

Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ayanlade Olayinka, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun haɗa baki da wasu mutum biyu wajen sayar da jaririyar.

A cewar sanarwar, lamarin ya fara bayyana ne bayan Mary Amos, kakar jaririyar, ta kai rahoton ɓacewar jikarta da aka haifa a Asibitin Ebepraise a ranar 6 ga Satumba, 2026.

Sanarwar ta ce lokacin da jami’an ’yan sanda suka fara bincike, Cecilia ta kasa bayar da cikakken bayani kan yadda jaririyar ta ɓace.

Advertisement

Binciken ya kai ga gano cewa ana zargin likitan, mahaifiyar jaririyar da wani mutum mai suna Hassan Oludunni sun haɗa baki wajen sayar da jaririyar ga Odunayo Folawewo kan Naira miliyan biyu.

Rundunar ta ce an raba kuɗin da aka samu, inda Cecilia ta karɓi Naira miliyan ɗaya, yayin da likitan da Hassan Oludunni suka karɓi Naira 500,000 kowannensu.

Kakakin rundunar ya ce jami’an ’yan sanda sun yi nasarar ceto jaririyar.

Ya ƙara da cewa likitan da Cecilia suna tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Rundunar ta ce tana ƙoƙarin cafke Hassan Oludunni da Odunayo Folawewo, waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, domin su fuskanci shari’a.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending