News
Dakarun Soji Sun Ceto Wanda Aka Yi Garkuwa Da Shi, Sun Kwato Naira Miliyan 10 A Kano
Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun ceto Alhaji Kabiru Aliyu, wanda aka yi garkuwa da shi a Jihar Kano, tare da kashe wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma kwato naira miliyan 10 da aka biya a matsayin kuɗin fansa.
An gudanar da samamen ne a dajin Falgore da ke Ƙaramar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan masu garkuwa da mutane a yankin.
Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 27 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina
Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Birged ta 3, Manjo Babatunde Zubairu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Sanarwar ta ce an yi garkuwa da Aliyu ne a ranar 11 ga Oktoba, 2026, a ƙauyen Fanyabo da ke dajin Falgore, lokacin da yake dawowa daga Kasuwar Yandoka a Jihar Kaduna.
Bayan sace shi, masu garkuwar sun tuntubi iyalansa da ke ƙauyen Yan Taburmi, inda suka buƙaci a biya kuɗin fansa domin sakin sa.
A cewar sanarwar, bayan samun sahihan bayanan sirri, dakarun sojojin sun shirya kwanton ɓauna tare da haɗin gwiwar jami’an ’yan sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da mafarautan yankin.
A yayin samamen, jami’an tsaron sun yi nasarar ceto wanda aka sace, tare da kashe mutum biyu da ake zargi mambobi ne na ƙungiyar masu garkuwa da mutane, yayin da wasu suka tsere zuwa cikin dajin.
Binciken da jami’an tsaron suka gudanar bayan samamen ya kai ga gano naira miliyan 10 da aka biya a matsayin kuɗin fansa, inda aka mayar da kuɗin ga Aliyu da iyalansa.
Kwamandan Birged ta 3 ta Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Saka Jimoh, ya yaba wa dakarun bisa ƙwarewa da jajircewar da suka nuna wajen gudanar da aikin.
Ya kuma tabbatar da aniyar rundunar na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin murƙushe masu aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Haka kuma, ya yi kira ga al’ummar yankin da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen yaƙi da miyagun laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
-
News5 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News2 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News12 hours agoƘungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
