News
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada matsayinsa na cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, yana mai cewa bai yi nadamar cire tallafin tun ranar farko ta hawansa mulki a watan Mayun 2023 ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 19 ga Oktoba, 2026, yayin wani taron siyasa da ƙungiyar City Boy Movement ta shirya a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
Shugaban ƙasar ya ce da a ce har yanzu Nijeriya na ci gaba da biyan tallafin man fetur, da tuni nauyin basussukan ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasar, yana mai cewa babu sauran ƙarfin da gwamnati za ta iya ci gaba da biyan tallafin.
Ya yi amfani da wani labari da ke cikin Littafi Mai Tsarki da Alƙur’ani wajen kwatanta yiwuwar dawo da tallafin da komawar Annabi Musa zuwa Masar ƙarƙashin mulkin Fir’auna bayan ya kuɓutar da mutanensa daga zaluncin Fir’auna.
“Ba za ku iya neman Musa ya koma Masar ba. Da ƙarfinku da goyon bayanku, ba za mu sake komawa Masar ba. Babu nadama,” in ji Tinubu.
Shugaban ƙasar ya yi wannan furuci ne yayin da wasu fitattun ‘yan siyasa na hamayya, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ke bayyana ra’ayoyinsu kan yiwuwar dawo da wani nau’i na tallafin man fetur.
Cire tallafin man fetur na daga cikin manyan manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, matakin da ya haifar da sauye-sauye a farashin man fetur da tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.
-
News7 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News4 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News3 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
